Home Labaru Karar-Kwana: Maniyyatan Nijeriya Shida Sun Rasu A Kasar Saudiyya – NAHCON

Karar-Kwana: Maniyyatan Nijeriya Shida Sun Rasu A Kasar Saudiyya – NAHCON

393
0
Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON
Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON

Hukumar kula da harkokin aikin hajji ta Nijeriya NAHCON, ta ce maniyyatan Nijeriya shida ne su ka rasu a kasar Saudiyya.

Kwamishinan Gudanarwa na hukumar Abdullahi Modibbo

Kwamishinan Gudanarwa na hukumar Abdullahi Modibbo Saleh ya shaida wa manema labarai cewa, dukkan maniyyatan da su ka mutu lokacin su ne ya yi.

Ya ce kimanin mutane 45,000 ne su ka isa kasar domin gudanar da aikin Hajjin bana, wadda ake sa ran akalla mutane miliyan biyu daga sassan duniya daban-daban za su gudanar da ibadar, wanda shi ne taron jama’a mafi girma a fadin duniya.

Modibbo ya kara da cewa, akwai kimanin maniyyata 300 daga jihar Kano da ba za su samu damar yin aikin ibadar ba saboda matsalolin sufuri.

Aikin hajji dai na daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar, wanda a kowace shekara miliyoyin Musulmi daga sassa daban-daban na duniya kan hallara a kasar Saudiyya domin aiwatarwa.

Leave a Reply