Bincike ya nuna cewa, akalla jiragen ruwa 10 za su iso tashoshin ruwa daban-daban karshen wannan mako domin sauke man fetur a Nijeriya, bayan jirage 8 da suka sauke fetur a karshen makon nan.
Jimaillar Jiragen 18 na dauke da ton 357,396 na man fetur, wanda za su kai jihar lagos.
A wata sanarwa da hukumar jiragen ruwa ta kasa ta fitar ta ce daya daga cikin jiragen ya sauke man fetur a ranar litinin din da ta gabata.
A bangare guda kuwa, Gwamnatin tarayya ta sake bayyana kudurin ta a kan batun da ya shafi janyen tallafin man fetur, inda ta ce ba ta da niyyar yin hakan a nan kusa da kuma nesa.