Gwamnatin tarayya ta bada umarnin kulle ofisoshin jakadancin ta da ke wasu kasashen duniya hudu sakamakon matsalar karancin kudade da gwamnati ta ke fuskanta.
Ministan kula da harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya bayyana haka, inda ya ce kasashe sun hada da Srilanka da Serbia da Ukraine da Czech Republic.
Onyeam ya kara da cewa, matsalar kudi ta tilasta wa gwamnati rufe wadannan ofisoshi, wanda hakan ya sa bata iya samun damar kulawa da ayyukan sun a yau da kullum.