Home Labarai Karancin Albashi: ‘Ƴan Ƙwadago Sun Fara Yajin Aiki A Najeriya

Karancin Albashi: ‘Ƴan Ƙwadago Sun Fara Yajin Aiki A Najeriya

137
0
Screenshot 2024 05 31 6.08.36 PM
Screenshot 2024 05 31 6.08.36 PM

Ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun shiga yajin aiki a yau Litinin

bayan an gaza cimma matsaya kan ƙarancin albashin ma’aikata tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnati.

Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci ma’aikatan lafiya, da na bankuna, da na jirgin sama da sauran ɓangarorin gwamnati su jingine aiki.

Haka nan ƙungiyoyin ƙwadagon sun buƙaci gwamnati ta soke ƙarin kuɗin lantarki da ta yi a watan da ya gabata.

Gwamatin Najeriya ta bayyana yajin aikin a matsayin haramtacce.

Tun bayan hawansa kan mulki, Tinubu na ta ƙoƙarin ganin ya rage tallafin da gwamnati ke bayarwa a ɓangarori daban-daban.

Sai dai tashin farashin kayan masarufi da zubewar darajar naira ya tsoma al’umma cikin ƙunci.

Leave a Reply