Home Home Karancin Abinci Na Kara Tsananta A Arewa Maso Gabas – MDD

Karancin Abinci Na Kara Tsananta A Arewa Maso Gabas – MDD

144
0

Majalisar Dinkin Duniya, ta koka da yadda ta ce rikicin Boko Haram ya maida mata da dama marasa galihu, musamman ta bangaren karancin abinci a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Babban Jami’in Majalisar a Najeriya kuma mai kula da ayyukan jin-kai Matthias Schhmale ya bayyana haka, inda ya ce rikicin ya fi kamari musamman ga marasa galihu da kananan yara.

Mista Matthias ya bayyana haka ne, lokacin da ya ziyarci sansanin El-Miskin da ke Maiduguri a Jihar Borno, inda ya ce ya tarar da kimanin ‘yan gudun hijira dubu 7 da 200 da su ka nemi mafaka a wajen.

Ya ce yanayin abinci ya yi tsanani ga iyalai da dama a sansanin saboda rashin kudaden gudanar da ayyuka.

Jami’in ya kara da cewa, mata sun shaida ma shi cewa sama da watanni uku ba su samu tallafin abinci ba, kuma su na kokawa da yadda za su ciyar da iyalan su.

Leave a Reply