Home Labaru Karamci: NAHCON Ta Karrama Limamin Daya Ceci Kiristoci 300

Karamci: NAHCON Ta Karrama Limamin Daya Ceci Kiristoci 300

281
0
Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON
Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta karrama wasu Musulmai ‘yan Najeriya guda biyu da suka nuna kyawawan halaye a yayin aikin Hajjin bana.

Hukumar ta ce mutanen biyu sun hada da Imam Abubakar Abdullahi, limamin wani Masallaci dake jihar Filato wanda ya ceci wasu kiristoci ‘yan kabilar Berom fiye da 300 daga harin yan bindiga, da kuma kofur Bashir Umar, Sojan da ya tsinci naira miliyan 15 kuma ya mayar.

Hukumar NAHCON ta karrama Imam Abubakar ne ta hanyar sanyashi cikin tawagar Malaman Hajji ta kasa da za su gudanar da wa’azin tunatarwa ga mahajjatan Najeriya a yayin aikin Hajji.

Haka zalika hukumar ta karrama Kofur Bashir Umar ta hanyar sanyashi daga cikin jami’an kwamitin tsaro na hukumar da za su kula da tsaron alhazan Najeriya da dukiyoyinsu a yayin zamansu a kasar Saudiyya.