Home Home Kano: PDP Ta Gargadi Ganduje Da Kada Ya Tatsi Masu Makarantu Kudade...

Kano: PDP Ta Gargadi Ganduje Da Kada Ya Tatsi Masu Makarantu Kudade Kan Lasisi

109
0

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kano ta yi kira ga gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kada ya sake ya yi amfani da batun soke rijistar makarantu masu zaman kansu wajen tatsar kudade daga masu makarantun.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na jihar, Shehu Wada Sagagi, wadda a ciki take nuna alhini bisa kisan yarinyar nan ‘yar shekara biyar Hanifa Abubakar wadda shugaban makatantarsu ya sace tare da kashe ta, jam’iyyar ta kuma yaba wa jami’an tsaro kan yadda suka yi saurin ganowa tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a lamarin a gaban kotu.

A kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na soke lasisin gudanarwa na dukkanin makarantu masu zaman kansu a jihar ne sakamakon abinda ya faru a kan yarinyar, jam’iyyar PDP  ta ce duk da cewa abu ne da yake da kyau sake tsarin makarantun, amma ta yi gargadi ga gwamnatin da kada ta yi amfani da wannan dama wajen tsatsar kudade daga masu makarantun.

Jam’iyyar ta bukaci gwamnatin jihar karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje da ta bi ka’idojin da doka ta gindaya na sanya ido tare da gudanar da makarantu masu zaman kansu wajen aiwatar da gyare-gyaren.