Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya ce zai raba wa mata masu juna biyu maganin cuta mai karya garkuwar jiki kyauta a jihar Bauchi.
UNICEF, ta ce za a raba magungunan ne a duk cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko guda 323 da ke fadin jihar.
Asusun, ya ce ya yi wannan tanadin ne, ganin cewa cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko a jihar su na kula da mata masu juna biyu kyauta.
Shugaban hukumar a Nijeriya reshen jihar Bauchi Bhanu Pathak, ya ce UNICEF ta yi haka ne domin kawo karshen yadda mata ke yawaita haihuwar jarirai dauke da cutar.
You must log in to post a comment.