Home Labaru Kalubalen Tsaro: Majalisar Dattawa Na Neman Hanyar Dakile Amfani Da Wayoyi Wajen...

Kalubalen Tsaro: Majalisar Dattawa Na Neman Hanyar Dakile Amfani Da Wayoyi Wajen Aikata Ta’addanci

306
0

Majalisar Dattawata nemi kwamitinta kan bin ka’idoji da sadarwa da ya gayyaci Ministan Sadarwar da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Pantami, domin ya zo ya yi mata cikakken bayanin yadda a ka yi ’yan ta’adda ke samun damar sheke ayarsu ta kafafen sadarwa da kuma amfani da na’urorin sadarwa wajen tafka ta’asarsu.

Majalisar ta ce, da yawan masu garkuwa da mutane su na amfani da layukan waya da wayoyin sadarwa wajen tattaunawa da iyalan wadanda suka sace domin neman kudin fansa, don haka ne majalisar ta ce akwai bukatar samun bayanin irin sakacin da a ke yi da wannan fanninin domin daukan matakan da suka dace a kai.

Matakin na zuwa ne bayan da aka gabatar da kuduri kan tabarbarewar tsaro, kudurin wanda mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sanata Emmanuel Bwacha na jam’iyyar PDP, mai wakiltar mazabar Taraba ta Kudu ya gabatar a gaban majalisar

Sanata Bwacha ya kara da cewar matsalar tsaro ba kawai ya karu ba ne a fadin kasar nan, ya na mai neman wuce makadi da ruwa ne sakamakon halin da ake ciki na tabarbarewar tsaro da jama’a ke kara shiga taraddadi a kulli yaumin,

A cewarsa, ‘yan matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, aikace-aikacen ‘yan bindiga, kisan kai da wasu matsalolin tsaro su kara ta’azzara a fadin kasar nan.

Leave a Reply