Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kalubalen Tsaro: Gwamnonin Jihohin Arewa Sun Yi Yi Ganawa Ta Musamman

Northern governors

Northern governors

Gwamnonin jihohin arewa sun sake bayyana damuwarsu kan salwantar rayukan
jama’a dake cigaba da ta’azzara a yankin

Taron gwamnonin da ya gudana a birnin Abuja, ya kuma jinjinawa gwamnatin tarayya a kan sabbin matakan da take dauka wajen samun nasarar yakin da ake yi da ta’addanci da kuma ‘yan bindiga tare da masu garkuwa da mutane.


Yayin mahawara a kan yanayin da yankin arewa ke ciki, gwamnonin sun sake daga muryar su a kan barazanar da ake fuskanta na samun miliyoyin yaran da basa zuwa makaranta, abinda ya sa suka yanke hukuncin kara zuba kudade wajen samar da ingantaccen ilimi da sana’oi da kula da lafiyar al’umma da kuma samar da kayan more rayuwa.


Sanarwar bayan taron gwamnonin da ya gudana a karkashin shugabancin gwamnan Gombe, Alhaji Inuwa Yahya yace sun karbi rahoto a kan shirin bunkasa ilimin mata dake gudana a wasu jihohin arewacin kasar nan da ake kira AGILE wanda ke gudana da tallafin Bankin Duniya, inda suka bayyana gamsuwa da tasirin shirin da kuma alkawarin bada gudumawar da ake bukata daga nasu bangaren.


Taron gwamnonin ya kuma karbi tawagar shugaban kungiyar tuntiba ta arewa  da ake kira ACF, inda bangarorin biyu suka yanke hukuncin yin aiki tare da kuma magana da murya guda domin kare muradun yankin.

Exit mobile version