Gwamnatin Zamfara ta bayyana dalilan da suka sa har yanzu ba dawo da layukan sadarwa ba a jihar.
Wata Sanarwar da kwamishinan watsa labaran jihar Ibrahim Dosara ya fitar ta ce umarnin da gwamnan jihar ya bayar na dawo da layukan sadarwar yana nan amma sanarwar ta faɗi hanyoyin da ta ce ake bi domin dawo da hanyoyin sadarwar.
A cewar gwamnatin Zamfara, matakan sun haɗa da tsarin doka da sa hannu kan umarnin wanda zai ba da izinin sa ke dawo da layukan sadarwar.
Har ila yau za’a yi nazari kan yanayin tsaro a ƙananan hukumomi 14 na jihar don tabbatar da irin shirye-shiryen da za a yi bayan dawo da hanyoyin sadarwar.
Sanarwar ta kara da cewa “Dole sai buƙatar daga ministan sadarwa da hukumar NCC ta dace da rahoton tsaro da sauran matakan da suka dace”.