Home Labaru Kalubalen Tsaro: Akpabio Na Shan Caccaka Kan Batun Kisan Sojoji A Delta

Kalubalen Tsaro: Akpabio Na Shan Caccaka Kan Batun Kisan Sojoji A Delta

85
0

Kungiyoyin fararen hula da masu sharhi kan harkokin tsaro sun
caccaki Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio.
Sanata Akpabio na shan caccakar ne kan kalaman da ya yi na
cewa yana zargin ba ’yan kasar nan ba ne suka yi wa sojoji kisan
gilla a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Jihar Delta.


An jiyo Sanata Akpabio na cewa, “Fatan da ya kamata mu yi yanzu shi ne a tsaurara bincike kan gaskiyar waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki. Ya ce a saninsa mutanen Delta na mutunta duk mai sanya kayan sarki, don haka ba zan so tashi guda in yarda cewa ’yan wannan yankin ne za su rufe idonsu su kashe sojojin Najeriya ba.”


Da yake martani ga kalaman na Sanata Akpabio, Auwal Musa Rafsanjani, babban darakta a Cibiyar Bayar da Shawarwari kan Dokokin da za su shafi Jama’a (CISLAC) ya ce kalaman abun Allah wadai ne.


Babban darakta a CLEEN Foundation, Gad Peter cewa ya yi, ya kamata masu riƙe da muƙamai na siyasa su riƙa sanya wa bakinsu linzami idan an samu faruwar irin wannan mummunan lamari

Leave a Reply