Rubutawa: Jibril Ibrahim
Fassarawa: Aliyu Abdullahi Gora II
Babu zato babu tsammani, Nijeriya ta fada cikin matsalar tabarbarewar tsaro, kusan a kowane bangare na kasar nan.
Shekaru bakwai da su ka gabata, mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro a wancan lokacin Kanar Sambo Dasuki, ya ankarar da kasar nan game da barazanar tsaro, lamarin da ya sa aka tura bataliyoyin dakarun soji zuwa jihohi 34, daga cikin 36 da ke fadin Nijeriya.
Karanta Labaru Masu Alaka: Mahimmancin Tsaro Da Yaki Da Cin Hanci – Dan Agbese
Tun daga wanacan lokacin, al’amarin sai ma ya kara ta’azzara, musamman ta yadda kanana da manyan makamai su ka yawaita a hannayen mutane, kuma wadannan makamai, babu masu amfani da su illa ‘yan ta’adda, da gaggagan masu aikata manyan laifuffuka, da masu amfani da su ta fuskar tada rikicin kabilanci ko addini, kawai da nufin kashe ‘yan Nijeriya.
Sakamakon haka, al’ummomi da dama, su ka dauki matakin yi wa kan su kiyamullai, ta hanyar samar da kungiyoyin tsaro na sa-kai, domin kare rayukan su da dukiyoyin su.
Babu wanda zai iya cewa uffan, ko kuma daukar wani mataki a kan gazawar jihohi da hukumomin da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ya rataya a wuyan su.
Wani abu da ke kara rura wutar barazanar tsaro kuma ita ce, kalaman batanci da sauran miyagun maganganu da su ka mamaye kafafen sadarwa na zamani.
Karanta Labaru Masu Alaka: Budaddiyar Wasika, Zuwa Ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
A yau, an wayi gari manoma ba su iya zuwa gonakin su, lamarin da ka iya haddasa matsalar fari a cikin ‘yan watanni kadan masu zuwa.
Ba karamin kalubale ba ne, ganin yadda gwamnatoci a dukkan matakai, ba su dauki matakin ba wasu bangarori kulawar da ta dace ba, wanda hakan ya sa wasu ke ganin kawai wata manuniya ce, da ke ankarar da jama’a su tashi tsaye, kowa ya yi sallah da karatun kan sa.
Wannan ya na daga cikin dalilan da su ka sa hukumar bincike da ci-gaban yankin arewa ARDP, tare da hadin gwiwar Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello, da Cibiyar harkokin Difilomasiyya ta Savannah, da kungiyar tabbatar da tasarin Dimokradiyya da ci-gaba, da hadakar kungiyoyin matasan arewacin Nijeriya, su ka shirya taron kwanaki biyu, domin lalubo hanyoyin samar da tsaro da sauran harkokin ci-gaba, wanda ya gudana a ranakun 1 da kuma 2 ga watan Yuli a garin Kaduna.
Taron dai ya maida hankali ne kacokam, a kan yadda al’ummomin yankin arewa za su yi nazari, a kan matakan da ya kamata su dauka, domin kare kawunan su, tare da inganta matakan wanzar da zaman lafiya.
Mutane masu kishi da kuma masana harkokin tsaro da dabaru, da kuma ilimin tattara bayanan sirri, sun gabatar da bayanai, a kan hanyoyin da ya kamata a bi, na samar da dabarun inganta tsaro a fadin Nijeriya.
Haka kuma, taron ya zayyana wasu matsaloli, wadanda ke bukatar kwararrun masu ruwa da tsaki su hada hannu, su lalubo hanyoyi da matakan da ya kamata a dauka, sannan su gabatar da rahoton su.
Matsalolin kuwa, sun hada da ta’addcin Boko Haram, da rikicin kabilanci da na addini, da rikice-rikice a kan iyakoki, da na garkuwa da mutane, da fashi da makami, da rigingimun ‘yan sara-suka a birane, da tu’ammali da miyagun kwayoyi, da harkokin difilomasiyya a tsakanin Nijeriya da makwaftan ta, irin kasashen Nijar da Kamarun, da Chadi, da kuma Benin.
Har ila yau, taron ya ja hankali da cewa, Arewa da ma Nijeriya baki daya, akwai matsalolin da su ka taimaka, wajen haddasa matsalar tashe-tashen hankula.
Karanta Labaru Masu Alaka: Mahimmancin Tsaro Da Yaki Da Cin Hanci
Bidiyo: Tsokaci: Mahimmancin Tsaro Da Yaki Da Cin Hanci
Talauci dai ya yi wa mutane katutu tsawon shekaru, ya hana su sha rawar gaban hantsi, yayin da hadamar mutanen da su ka kware a bangaren satar dukiyar al’umma, ta haddasa bacin rai a zukatan mutane.
Arewacin Nijeriya ya fi kowane bangare yawan al’umma, musamman ta yadda ake samun karanci, mace daya ta haifi ‘ya’ya bakwai, kuma hakan ya bada gudunmuwa wajen assasa matsalar rashin guraben aiki a tsakanin matasa, lamarin da ya sa matasa ke kaurace wa kauyukan su na karkara, su shiga birane domin neman abin yi.
Duk wadannan matsalloli na rashin tsaro sun samo asali ne tun daga gidajen iyalai, musamman, ta yadda talauci ke tilsta wa magidanta tura ‘ya’yan su maza uwa-duniya da sunan almajiranci, ko kuma aurar da ‘ya’yan su mata tun ba su san mecece balaga ba.
Wadannan yara da ake yi wa auren wuri, kan ka ce kwabo sun cika gida da ‘ya’ya, ga shi kuma ba su mallaki hankalin da za su iya rike gida a matsayin matan aure ba, kuma hakan, ya kan haddasa yawaitar mutuwar aure, tare da haddasa gasar yawan aurace-aurace tsakanin mazaje, da kuma yawaitar zawarawa a kan tituna.
Har ila yau, wanzuwar sabbin akidodjin addini ta bada gudunmuwa, ta yadda mafi yawan matasa, ba daga gida ko kuma hannun sannanun malaman yankunan su su ke samun ilimi ba, lamarin da ake ganin ya na janyo wasu bakin munanan dabi’u, har ta kai ga ‘ya’ya su daina ganin kimar iyayen su da shugabannin su na gargajiya, kuma wannan ya na daga cikin dalilan da su ka sa aka sha ganin yadda wasu matasan da su ka rungumi Ta’addancin Boko Haram, ke yi wa iyayen su yankan rago kamar dabbobi.
Sannan tsarin zamantakewa musamman ta fuskar abin da ya shafi kan iyakoki a yankunan Arewa ta tsakiya da Arewa maso yammacin Nijeriya, shi ma ya taka gagarumar rawa ta wannan fuska.
Haka kuma, gurbacewar zamantake wa a tsakanin al’umma ta taimaka ainun, musamman ta yadda masu hannu da shuni kawai ke iya daukar dawainiyar karatun ‘ya’yan su, talakawa kuma, ko oho.
Sannan da yawa masu hannu da shuni, ba su ma da masaniya a kan irin rayuwar da al’ummomin su ke ciki, kuma mafi akasari, zaman doya da manja ake yi a tsakain su, musamman sakamakon bullar yawaitar dabi’ar tu’ammali da miyagun kwayoyi.
Wannan ya na nuni da cewa, matsalolin ba su tsaya a kan lamarin tsaro kawai ba, dole a tashi tsaye domin lalubo hanyoyin samun mafita, kuma kananan yara miliyan 13 da dubu 200 da aka ce ba su zuwa makaranta a yankin arewa, a tabbatar an ba su ilimin da ya dace.
Kuma dole a dubi lamarin almajiranci tare da daukar mataki, a kuma dakile dabi’ar yi wa kananan yara mata auren wuri, sannan a tura su zuwa makarantu, har su kai shekaru 18 da haihuwa. Wannan shi ne abin da ya fi dacewa, sannan iyaye da malaman addini, da sarakunan gargajiya, su na da gagarumar rawar da za su taka, a bangaren samar da tsaro a tsakanin al’ummomin su.
Ta’addancin Boko Haram dai ya dade ana fama da shi a kasar nan, kuma duk da ikirarin cewa ana samun galaba a kan su, har yau ba su daina yi wa mutane illa ba.
Amfani da dakarun soji kadai ba zai wadatar ba, kuma matsalar ta’addancin masu tsattsauran ra’ayin addini, na iya daukar tsawon lokaci ana fama da ita, matukar hukumomin kula da harkokin addinai ba su dauki kwararan matakan da su ka dace ba.
Haka kuma, inganta alaka tsakanin sojoji da al’umma ta na da matukar mahimmanci, ta yadda mutanen gari za su sa mu sakin fuskar da za su iya bada gudunmuwa, musamman a bangaren samar da bayanan sirri tsakanin su da jami’an tsaro, domin tsaro lamari ne da ya shafi kowa, don haka ya zama dole al’umma su tashi tsaye su nemi hanyoyin kare kawunan su daga ta’addancin ‘yan ta’adda.
Daya daga cikin manyan kalubalen da yankin arewacin Nijeriya ke fuskanta ita ce, ta yadda ba a bada sahihan labarai game da duk rikicin da ya afku, musamman abin da ya shafi addinin Musulunci da na Kirista.
Misali, rikicin da ya afku a jihar Taraba tsakanin Musulmi da kirista kwanan baya, kafofin yada labarai sun yi wa lamarin ca, amma da aka samu rikici tsakanin al’ummomin TV da Jukun wadanda duk kirista ne, sai ‘yan jarida su ka yi gum da bakin su, kamar yadda ba su damu da yada labarai a kan kashe-kashen da ke addabar jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina ba.
A gaskiya, ya zama wajibi al’ummomin yankin arewacin Nijeriya su tashi tsaye, su lalubo hanyoyin magance matsalolin tabarbarewar tsaro da ke addabar yankin a kowace rana, musamman ta hanyar wayar da kawunan al’umma, da hanyoyin daukar mataki a kan ayyukan ta’addancin da ke ci-gaba da ta’azzara.
‘Yan sandan Nijeriya dai, sun karkata ne kawai wajen ba masu hannu da shuni kariya, domin su na da abin biya. Jami’an ‘yan sanda sun zama abokan masu hannu da shuni, ba abokan kowa kamar yadda ake cewa a baya ba, don haka ya kamata kowace al’umma ta yi tunanin hanyar da za ta bi, domin sama wa kan ta mafita game da ayyukan ta’addanci.
Ya zama wajibi dai a kara inganta hukumomin tsaro, tare da magance matsalar yawaitar makamai a hannun mutane, yayin da ya zama dole a samar hanyoyin tattaunawa tsakanin al’umma da gwamnatocin tarayya da na jihohi, domin lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya, da kare rayuka da dukiyoyin mutane, da kuma yadda za a bullo wa ayyukan ta’addanci ta bayan gida.
A karshe, dukkan mu muna da alhakin bada gagarumar gudunmuwa, musamman ta fuskar dakile dabi’ar amfani da kalaman batanci, ko yada munanan bayanai a shafukan sada zumunta na zamani, domin wanzar da dawwamammen zaman lafiya, a stakanin alummomin kasar nan.