Home Labaru Kiwon Lafiya Kalubale: Alkalami Ya Bushe Dangane Da Hana Kiwo A Kudancin Nijeriya –...

Kalubale: Alkalami Ya Bushe Dangane Da Hana Kiwo A Kudancin Nijeriya – Akeredolu

103
0
Oluwarotimi-Akeredolu

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya ce alkalami ya bushe dangane da dokar da gwamnoni su ka amince ta hana yawon kiwo, wadda za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, kuma duk wanda aka samu ya na yawon kiwon zai fuskanci hukunci.

Akeredolu ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke ganawa da sabon mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya Ene Okon da ya ziyarce shi a birnin Akure.

Ya ce sun dauki matakin hana yawon kiwon ne domin kawo karshen rikicin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya, yayin da ya kare matakin kafa rundunar tsaro ta Amotekun da ya ce an kafa ta ne domin taimakawa wajen samar da zaman lafiya.

Sabon mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya Ene Okon, ya yaba wa gwamnan saboda jajircewar sa wajen kafa rundunar Amotekun domin samar da tsaro.

Ya ce ya na da masaniyar jihar Ondo na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar rikicin manoma da makiyaya, amma yanzu labarin ya sauya saboda zaman lafiyar da aka samu, lamarin da ya rage nauyin da ke wuyan jami’an ‘yan Sanda da sauran hukumomin tsaron da ke aiki a jihar.