Home Labaru Kaduna: An Gano Wace Baturiyar Da Masu Garkuwa Suka Kashe

Kaduna: An Gano Wace Baturiyar Da Masu Garkuwa Suka Kashe

487
0

An gano wace ce Baturiyar da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka kashe a karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

An bayyana cewar matar mai suna Faye Money, ‘yar asalin kasar Ingila ce dake aiki da wata kungiya  mai sana Mercy Corps a Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya bayyana hakan a dandalin sada zumunta na WhatsApp mallakar rundunar ‘yan sanda, ya ce rundunar na iya bakin kokarinta domin kubutar da ragowar mutanen da aka sace.

A ranar juma’a da ta gabata ne wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane suka kai harin, kan mai uwa da wabi’ da a Kajuru.Wani kusanci ga shugaban karamar hukumar Kajuru ya shaida cewar masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da mutane biyar.

Leave a Reply