Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kada Kuri’a Daga Ketare: Ƙudurin Zaɓe Dake Gaban Majalisa Ya Tsallake Karatu Na Biyu

Nigeria House of Representatives REPS

Nigeria House of Representatives REPS

Ƙudirin da zai yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima domin ba ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓe ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai a yau Laraba.

Ƙudirin wanda shugaban majalisar, Abbas Tajudeen da Sodeeq Abdullahi suka ɗauki nauyin sa, na neman yin gyara ga dokar zaɓe ta 2022 domin a bayar da dama ga ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje su kaɗa ƙuri’a.

An amince da karanta ƙudurin karo na biyu a watan Yuli, kuma an miƙa shi ga kwamitin da ke kula da harkokin zaɓe don ci gaba da nazarin sa.

Sai dai bayan tsallake karatu na biyu a ranar Talata, an miƙa shi ga kwamitin gyaran kundin tsarin mulki don ci gaba da tattaunawa a kan sa.

Exit mobile version