Home Labaru ‘June 12’: A Daina Karɓo Umarni Daga Kotu Don A Gurgunta Dimokraɗiyya’...

‘June 12’: A Daina Karɓo Umarni Daga Kotu Don A Gurgunta Dimokraɗiyya’ – Tinubu

185
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ja kunnen musamman
‘yan siyasa su guji zuwa kotuna domin biyan buƙatun kan su,
ta hanyar karɓo umarnin kotu da nufin gurgunta
dimokraɗiyya.

Tinubu ya ce a fili ya ke cewa, akwai masu zuwa kotu su na karɓo umarnin da bai zama dole ba kuma ba bisa ƙa’ida ba, don kawai su janyo wa dimokraɗiyya cikas, don haka ya ce ba za su lamunci masu irin wannan baƙar aniyar ba.

Da ya ke magana kan zaɓen shekara ta 2023, Tinubu ya yi jirwaye mai kama da wanka ga waɗanda ke shari’a da shi a kotu, inda ya ce duk waɗanda ba su iya jure zafin faɗuwa zaɓe ba, ba su cancanci jin daɗin samun nasara ba idan nasara ta juyo kan su.

Shugaba Tinubu ya hori ‘yan Nijeriya su daure su bi shi kada su karaya, domin hanyar da zai bi da su mai ɓullewa ce.

Leave a Reply