Home Labaru Kiwon Lafiya Jita-Jita: Fadar Shugaban Kasa Ta Musanta Cewa Wani Hadimi Ya Kamu Da...

Jita-Jita: Fadar Shugaban Kasa Ta Musanta Cewa Wani Hadimi Ya Kamu Da Covid-19

242
0

Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da labarin da wasu kafafen yada labarai suka wallafa dake cewa Hadimi na Musamman kan Harkokin Cikin Gida ga Shugaba Muhammadu Buhari ya kamu da cutar coronavirus.

Sarki Abba (

Da yake karyata lamarin mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mallam Garba Shehu ya ce Sarki Abba bai kamu da cutar covid-19 ba.

Mallam Garba ya ce dukkan ma’aikatan da ke zagaye da kuma kusa da Shugaba Buhari, ana yi masu gwajin cutar akai-akai domin tabbatar da lafiyar Shugaban Kasa.

Ya ce Sarki Abba yana cikin sahun ma’aikatan da sakamakon gwajinsu bai taba nuna suna dauke da kwayoyin cutar ba.

Daga karshe ya bukaci Al’ummar kasar nan da kada su bari wata kafar watsa labarai ta jefa su cikin rudu ko yaudara musamman a yayin da suka kware wajen cin kasuwarsu ta hanyar wallafa rahotanni marasa tushe.