Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Jiragen Yakin Nijeriya Sun Yi Ruwan Wuta A Kan ‘Yan Boko Haram

Rundunar Sojan sama ta Nijeriya ta fara samun nasara a sabon salon yakin da ta kirkiro mai taken rawan mesa, wanda ta ce ta kirkiro shine domin ragargazar ‘yan Boko Haram.

Daraktan yada labarai na rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar, inda yac e sabon salon yakin ya fara samar da sakamakon da ake bukata.

Daramola ya ce, a ranar da suka kaddamar sabon salon, jiragen yakin su ya yi wa mayakan Boko Haram ruwan wuta , wanda hakan ya yi sanadiyar konewar wasu daga cikin su kurmus, tare da lalata sansanonin su a garin Parisu da Maloma da ke cikin dajin Sambisa.

Kamfanin dillancin labarun Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, kafin rundunar ta kaddamar da hare-hare sai da ta gudanar da bincike, lamarin da ya sa ta samun bayanan da ke tabbatar da taruwar ‘yan Boko Haram a sansanonin.

Daramola ya kara da cewa, sansanin Parisu sun gano ‘yan ta’adda 30 ta hanyar amfani da jirgin leken asiri, wanda hakan ya ba su damar yi masu luguden wuta da kunalalata maboyar su.

Exit mobile version