Shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya zargi kan sa game da jinkirin da aka samu wajen amincewa da kasafin shekara ta 2019 ba majalisar dokoki ta kasa ba.
Bayan ya sa hannu a kan kasafin shekara ta 2019 dai, shugaba Buhari ya tabbatar da rashin amanna a kan Dogara da Sanata Bukola Saraki.
Yakubu Dogara, ya ce tun daga lokacin da shugaba Buhari ya shiga ofis bai taba iya gabatar da kasafi a kan lokaci ba.
Ya ce Kasafin shugaba Buhari na farko shi ne na shekara ta 2016, wanda ya gabatar a ranar 22 ga watan Disamba na shekara ta 2015, kimanin kwana tara kafin karewar kasafin shekarar, kuma karancin lokacin da majalisar dokoki ke bukata don amincewa da kasafi watanni uku ne.
Dogara ya ce abin da ‘yan Nijeriya ba su sani ba kuma shugaba Buhari ba zai fada ba shi ne, majalisar zartarwa tare da hadin kan ma’aikatu sun cigaba da bada shawarar kara tulin ayyuka a kasafi shekara ta 2018 har zuwa watan Afrilu da Mayu, lamarin da ya yi sanadiyyar jinkirta amincewar kasafin shekara ta 2018.
You must log in to post a comment.