Home Home Jihohi 12 Da Abuja Da Za A Fuskanci Tsananin Zafin Rana —...

Jihohi 12 Da Abuja Da Za A Fuskanci Tsananin Zafin Rana — NIMET

8
0
Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya NiMet, ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin kasar nan.Z

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya NiMet, ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin kasar nan.Z

Ta ce mutane za su ji sauyin al’amurra a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar.

Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci karuwar yanayin zafin rana sun hada da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara, da birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma Borno.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a Abuja, ta ce ta lura da cewa yanayin zafin rana zai kai maki 40 a ma’aunin celcius a cikin kwanaki biyu masu zuwa.

Hukumar NiMet, ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun hada da wasu sassan jihohin Sokoto a Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa, sannan ta yi gargadin cewa jihohi irin su Bauchi da Gombe da Adamawa su na cikin hadarin rashin jin dadi musamman a bangaren lafiyar su.

A karshe Hukumar ta sharwarci mutanen da ke zaune a jihohin da abin zai shafa, su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin.