Home Labaru Ilimi JARABAWAR 2019: NECO TA SAYO NA’URA 8000 DOMIN TANTANCE DALIBAI

JARABAWAR 2019: NECO TA SAYO NA’URA 8000 DOMIN TANTANCE DALIBAI

1119
0
NECO

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantar sakandiri ta kasa NECO ta sayo na’ura guda 8000 wadanda za a yi amfani da su wajen tantance masu rubuta jarrabawar da hukumar ke shiryawa, sannan kuma za a yi amfani da su domin sanin yawan daliban da suka rubuta jarrabawar.

Shugaban hukumar gudanarwa ta NECOn Dakta Abubakar Sadik Muhammad, ya bayyana haka a shelkwatar hukumar da ke Minna.

Abubakar Sadik, ya ce wannan ya zama wajibi domin ganin an dakile masu shigar burtu suna rubutawa wadan su dalibai jarrabawa.

Ya kara da cewa, binciken da aka yi na baya-bayan nan ya nuna, wasu manyan mutane na daukar hayar wadanda za su rubuta wa ‘ya’yan su jarrabawar, wanda hakan na dada rage matsayin da jarrabawar ke da shi.

Ya ce, da wannan na’urar za a iya gano wadanda aka dauko su haya domin su rubutawa wasu jarrabawa.

Leave a Reply