Babban Hafsan rundunar sojin kasa ta Nijeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ce ya bada umarnin a sake bitar irin rawar da sojoiji za su taka yayin gudanar da zabubbukan Nijeriya a shekara ta 2023.
Janar Yahya ya bayyana haka ne, yayin wani taro da manyan kwamandoji da Hafsoshin soji a birnin Abuja, inda ya ce sanannen abu ne sojoji su rika bitar irin ka’idoji da tsarin rawar da su ke takawa yayin gudanar da ayyukan su gwargwadon yanayi da halin da ake ciki.
Ya ce wannan shi ne abin da ake yi domin tabbatar da gudunmuwar su wajen taimaka wa hukumomin fararen hula ta fuskar samar da zabe na gaskiya mai cike da adalci.
Babban Hafsan, ya ce ba su da alaka ta kusa ko ta nesa da ‘yan siyasa, muradin su kawai shi ne samar da taimako ga hukumomin fararen hula, sannan su koma gefe su cigaba da ayyukan su kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.
You must log in to post a comment.