Home Labarai Jam’iyyar PDP Za Ta Iya Nasara Ko Da Ba Tare Da Wike Ba...

Jam’iyyar PDP Za Ta Iya Nasara Ko Da Ba Tare Da Wike Ba – Atiku

64
0

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce Jam’iyar za ta samu nasara ba tare da gudumawar Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ba.

Atiku Abbakar ya bayyana haka ne, lokacin da ya gana da shugabannin kwamitin amintattu na Jam’iyar, wadanda ke kokarin sasanta barakar da aka samu tsakanin Atiku da Wike bayan zaben fidda gwanin da ya samu nasara.

Tun bayan zaben fidda gwanin da Atiku ya samu nasara, Wike da magoya bayan sa ke ci-gaba da korafi a kan zargin rashin adalci, yayin da su ka gindaya wasu sharudda masu tsauri da su ke bukata a biya masu kafin su goya wa Atiku baya.

Daga cikin bukatun ku akwai sauke shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu, domin maye gurbin sa da wani dan kudancin Nijeriya tunda dan takaran shugaban kasa ya fito daga yankin arewa, lamarin da wasu daga cikin ‘yan Jam’iyyar ke cewa ba zai yiwu ba.

Atiku Abubakar ya bada misali da zaben shekara ta 2019, inda ya ce duk da ya ke shugaba Buhari bai lashe zaben Jihar Rivers ba, nasarar da ya samu a Jihohin Lagos da Kano da wasu jihohi sun taimaka masa zama shugaban kasa.