Shugaban jami’ar Bayero da ke Kano Farfesa Muhammad Yahuza ya kori dalibai 63 tare da dakatar da wasu 13 har na tsawon shekara guda, sakamakon kamasu da laifin satar jarabawa.
Bayanin haka na kunshe ne a wata takardar da daraktar jarabawa na makarantar Amina Umar Abdullahi ta sa hannu ta kuma rabawa manema labarai a Kano.
A cewar ta, an dau wannan matakin ne sakamakon bukatar hakan da majalisar zartarwar makarantar ta gabatar a kan hukuncin satar jarabawa.
Kwamitin ladaftarwa na majalisar zartarwar ya gabatar da bukatar ne a taro majalisar na 374 wanda ya gudana a ranar 28 ga watan Agusta na shekara ta 2019.
Ta ce daliban da aka kora sun hada da dalibai goma, wadanda ba digirin farko suke ba, sannan wasu 10 daga makarantar cigaba da karatu da wasu 7 daga sashin kimiyyar kiwon lafiya da kuma 7 daga sashin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa.
Haka kuma, akwai wasu karin dalibai 6 daga cikin masu koyon karantar da malamai, wasu 6 kuma daga sashin karatun engineering da dai sauran su.