Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS, sun sake kama
dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin
Emefiele bayan hatsaniyar da su ka yi da jami’an gidan yari.
Lauyoyin Emefiele dsai sun shaida wa manema labarai a Legas cewa, sun bar jami’an hukumar DSS su kama wanda su ke karewa ne don gudun harbe-harbe tsakanin jami’an biyu.
Tun farko dai Kotun ta bada umarnin a cigaba da tsare Emefiele a Gidan Yarin Ikoyi da ke Legas, har sai ya cika sharuɗɗan belin sa da aka bada kan naira miliyan 20.
A wani bangare kuma, rahotanni sun ce takaddama ta barke tsakanin Jami’an hukumar tsaro ta DSS da na gidan yari, inda su ka ba Hammata iska a kan wanda ya fi dacewa ya cigaba da tsare Emefiele har zuwa lokacin da zai cika ka’idodin belin da kotu ta gindaya masa, sai dai a karshe jami’an hukumar DSS sun yi nasarar tafiya da tsohon gwamnan babban bankin.
Hukumar DSS dai ta tuhumi Emefiele ne da mallakar ƙaramar bindiga ba bisa doka ba, zargin da ya musanta.
Tuni dai Mai Shari’a Nicholas Oweibo ya ɗage zaman kotun zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.