Home Labaru Jami’An DSS Sun Yi Wa Ofishin EFCC A Lagos Dirar-Mikiya

Jami’An DSS Sun Yi Wa Ofishin EFCC A Lagos Dirar-Mikiya

1
0

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS, sun yi wa ofishin
hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC dirar-mikiya,
inda su ka hana jami’an EFCC shiga ofishin su da ke Ikoyi a
jihar Lagos.

Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa, tun farko akwai sabani tsakanin hukumomin biyu, a kan wani gini da kowane bangare ke ikirarin ya mallaka.

Wani jami’in hukumar DSS da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce sun dade su na takaddama da hukumar EFCC a kan wanda ya mallaki ginin, wanda hukumar DSS ke amfani da shi tun kafin a kirkiri hukumar EFCC.

Jami’in ya kara da cewa, batu ne da ya ke a tsakanin hukumomin biyu, kuma bai je gaban shari’a ba sannan ba su taba rikici a kai ba kafin yanzu.

Kokarin ji daga bakin masu magana da yawun hukumomin biyu a kan batun dai bai yi nasara ba.