Home Labaru Jakadanci: Bashar Al-Assad Da Sarkin Jordan Sun Yi Magana A Karon Farko...

Jakadanci: Bashar Al-Assad Da Sarkin Jordan Sun Yi Magana A Karon Farko Cikin Shekara 10

118
0

Shugaban Syria Bashar al-Assad da Sarkin Jordan Abdullah II sun yi magana ta waya bayan shekara 10.

Shugaban na Syria da shugaban na Jordan sun tattauna kan dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Wannan ce tattaunawa ta farko tsakanin bangarorin biyu tun shekarar 2011 da kuma fara yaƙin basasar Syria.

A yayin tattaunawar ta su, Sarki Abdullah II ya jaddada goyon bayan da Jordan ta ke bayar wa don tabbatar da ƴancin Syria da zaman lafiyar ta.

Jordan ta sake buɗe iyakar ta ta Jaber-Nasib wanda ke kusa da Syria a makon da ya gabata don ƙarfafa alaƙarta da Syria.