Home Labarai Jajircewa: Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Al’ummar Ƙasa

Jajircewa: Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Al’ummar Ƙasa

204
0
Wale Edun
Wale Edun

Gwamnatin tarayya ta ce tana yabawa da jajircewar ƴan ƙasa a daidai wannan lokaci da ake fama da matsaloli sanadiyar gyare-gyaren inganta tattalin arzikin ƙasa da ta ɓullo da su.

Ministan kuɗi da tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasa, Wale Edun ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa kwamitin harkokin kuɗi na Majalisar Dattawa jawabi.

Ya ce an kusa gama da shan wahalar, domin a cewar sa an fara ganin nasara a gyare-gyaren da aka ɗauko.

Ya ce a gyare-gyare guda biyu na farashin man fetur da kuɗaɗen ƙasashen waje sun fara haifar da da mai ido, dan haka akwai buƙatar a yabawa jajircewar ƴan Najeriya bisa abubuwan da suka jure domin samun wannan nasarar.

A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa ya ce sun zauna ne domin sanin ko gyare-gyaren da aka ɗauko suna aiki, ko akasin haka.

Leave a Reply