Sojojin kasar Chadi sun kama wasu makamai masu dumbin yawa a wata maboya da ake kyautata zaton rumbun ajiyar makaman mayakan kungiyar kungiyar Boko Haram ne da ke cikin dajin Sambisa.
Dakarun sojin kasar Chadi suka fara wani atisayen ba mutunci a kan mayakan kungiyar Boko Haram a yankin Goje zuwa yankin kasar Chadi a cikin dajin Sambisa, shelkwatar Boko Haram.
Sojojin kasar Chadi sun shafe sa’o’i kimanin hudu suna farautar mayakan kungiyar Boko Haram a wani atisaye da shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, ya jagoranta, wanda shi ma tsohon shugaban rundunar sojojin kasar Chadi ne.
Rumbun makaman da sojojin suka gano shi ne mafi girma da kungiyar Boko Haram ke gadara da shi.

