Home Labaru Inganta Tsaro: Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Ya Raba Wa ‘Yan Sanda Ababen...

Inganta Tsaro: Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Ya Raba Wa ‘Yan Sanda Ababen Hawa

665
0
Mohammed Adamu, Shugaban rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya
Mohammed Adamu, Shugaban rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Akalla jami’an ‘yan sanda da su ka kunshi jihohin Kano da Jigawa da Katsina 1,000 ne su ka samu babura da Keke Napep da shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu ya rarraba.

Shugaban ‘yan sandan, tare da hadin gwiwar kungiyar hadin kan ‘yan sandan yankin ne su ka raba baburan samfurin Bajaj da Keke Napep a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kungiyar ta shaida wa manema labarai cewa, burin ta shi ne tabbatar da walwalar jami’an tsaron ta hanyar magance kalubalen rashin ababen hawa da su ke fama da ita.

Yayin mika makullan ababen hawan ga jami’an da su ka samu, mataimakin shugaban ‘yan sandan yanki na daya Dan Bature, ya hori jami’an su maida alherin da aka yi masu ta hanyar jajircewa ga ayyukan su kamar yadda ya dace.

Leave a Reply