Shugaban rundunar sojin kasa Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce babban burin sa shi ne ya ga ya inganta rayuwar jami’an sojin Nijeriya.
Buratai ya kaddamar da wasu sabbin gidaje da hukumar ta gina a jihar Bauchi, domin sama wa jami’an ingantaccen muhalli, inda ya ce burin sa shi ne yaga ya inganta jin dadi da lafiyar jami’an sojin Nijeriya.
Janar Buratai ya kara da cewa, yanzu haka akwai ayyukan da ake gudanarwa a fadin Nijeriya, wadanda jami’an hukamar soji ne kawai za su amfana da su.
A karshe ya yi kira ga jami’an soji su ba sauran jami’an tsaron Nijeriya hadin kai, wajen gabatar da ayyukan da za su kawo ci-gaban kasa.
You must log in to post a comment.