Home Home INEC Ta Ware Manyan Lauyoyi Da Biliyoyin Kudade Domin Kare Sakamakon Zabe

INEC Ta Ware Manyan Lauyoyi Da Biliyoyin Kudade Domin Kare Sakamakon Zabe

1
0

Akalla manyan lauyoyi tara ne hukumar zabe ta nada, domin kare sakamakon zaben shugaban kasa na shekara ta 2023 a gaban kotu.

Babban lauya kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Nijeriya NBA, Abubakar Mahmud ne zai jagoranci tawagar kwararrun lauyoyin.

Sauran manyan lauyoyin sun hada da Stephen Adehi da Oluwakemi Pinheiro da Miannaya Essien da Abdullahi Aliyu.

Wata majiya ta ce, akwai manyan lauyoyi hudu da ke aiki a sashen shari’a na hukumar zabe da za su yi aiki a shari’ar, ciki kuwa har da Gaba Hassan da Musa Attah da Patricia Obi.

Hukumar zaben, ta kuma ware kudaden da yawan su ya kai Naira Biliyan 3 domin kare sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da na gwamnoni.