Home Labaru INEC Ta Sa Ranar Sake Sabon Zaben Sanata Dino Melaye

INEC Ta Sa Ranar Sake Sabon Zaben Sanata Dino Melaye

827
0
INEC Ta Sa Ranar Sake Sabon Zaben Sanata Dino Melaye
INEC Ta Sa Ranar Sake Sabon Zaben Sanata Dino Melaye

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta na duban yuwuwar sake zaben sanata Dino Malaye a ranar 16 ga watan Nuwamba wato ranar da za a yi zaben gwamnan jihar.

Kwamishinan zabe mai kula da jihohin Kogi da Nasarawa da Kwara, Muhammad Haruna ya bayyana haka ga manema labarai a Lokoja.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan ya soke nasarar sanata Dino Melaye da kotu ta yi, Haruna ya ce tunda akwai sauran kwanaki 34 a yi zaben gwamna, to akwai yuwuwar a hada da na sanatan.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ta ruwaito cewa, kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben sanata Melaye na jam’iyyar PDP, sannan kotun ta umarci hukumar INEC da ta yi sabon zabe a cikin kwanaki 90 da yanke wannan hukunci.

Hukuncin ya biyo bayan karar da Sanata Smart Adeyemi na jam’iyyar APC ya shigar a gaban kotu tun a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Kwamishinan INEC Muhammad Haruna ya sauka garin Lokoja domin gudanar taron gogar da manema labarai a kan yada labaran bogi, wanda  gidauniyar zabe ta duniya ta shirya tare da hadin guiwar INEC.