Home Labaru Ina Da Yakinin Samun Nasara A Kotu -Dan Takarar Gwamnan APC A...

Ina Da Yakinin Samun Nasara A Kotu -Dan Takarar Gwamnan APC A Bauchi

88
0

Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar APC
Sadique Baba Abubakar, ya nuna kwarin gwiwar cewa zai
samu nasara a kotun sauraren kararrakin zabe.

Sadique Baba Abubakar, ya ce a zaben da aka gudanar shi ne ya samu nasara, kuma ya na da tulin hujjojin da za su gabatar a gaban kotun.

Ya ce a yanzu sashen shari’a na Nijeriya ya inganta, don haka ya na da cikakken kwarin gwiwar za su wanzar da adalci da gaskiya a tsakani.

“Nasara a hannun Allah ya ke. Mun tabbatar zalumci aka yi kuma da izinin Allah, Allah zai kwato hakkin jama’a. Sannan mun tabbatar yanayin shari’a na Nijeriya na da kyau don mutane ne adilai wadanda za su tabbatar da gaskiya.”

Abubakar ya tabbatar da cewa, za su cigaba da neman hakkin su babu dare babu rana har sai sun tabbatar sun kwace mulki, ya na mai cewa ya na da kwarin gwiwar Allah zai kwato wa jama’a hakkin su domin shi ya san abin da ya faru a lokacin zaben, kuma sun tabbatar matakan da su ka dauka za su fito
da abubuwan da ake nema na ganin an kwato hakkin jama’a an dawo da shi.

Leave a Reply