Home Labaru Ilimi Ilimin Yanar Gizo: Hukumar NBAIS Ta Shirya Wa Ma’aikatan Ta Taron Bita

Ilimin Yanar Gizo: Hukumar NBAIS Ta Shirya Wa Ma’aikatan Ta Taron Bita

1580
0

Hukumar shirya jarabawar harshen larabci da addinin Musulunci ta kasa NBAIS, ta bukaci hukumomin gwamnati da sauran kamfanoni masu zaman kan su su rika horar da ma’aikatan su a kan yadda ake amfani da Na’ura mai kwakwalwa da yanar gizo domin gudanar da aikin su yadda ya kamata.

Jami’ar kula da sashen sarrafaNa’ura mai kwakwalwa da yanar gizo ta ma’aikatar Hajiya Rabi Muhammad Shehu ta bayyana haka,yayin wani taron karawa juna sani na kwanaki uku da hukumar ta shiryawa ma’ikatan ta a Kaduna. Rabi Muhammad, ta ce makasudin taron shine, kara zaburar da ma’aikatan sua kan yadda za su rika shirya wa dalibai jarabawa da sakin sakamakon ta a yanar gizo, wanda hakan zai ba daliban damar samun sakamakon su cikin sauki.

Ta ce taron zai kuma horar da ma’aikatan hukumar yadda ake gudanar da ayyuka a zamanance da kuma kara masu hazaka yadda ya kamata.

Rabi ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki a daukacin hukumomin Nijeriya su rika shiryawama’aikatan su irin wannan taro, domin ba su kwarin gwiwar aiwatar da aikin su cikin natsuwa ba tare da wata fargaba ba.

Leave a Reply