
Gwamnatin Najeriya ta sanar da fara neman ilimi ta intanet kyauta, wanda ake kira da “inspire.education.gov.ng” ya kuma shafi kowanne matakin karatu domin saukaka hanyar neman ilimi.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce shafin yanar gizon zai iya daukar ‘yan Najeriya miliyan biyu a lokaci guda.
Adamu Adamu ya kara da cewa an yanke shawarar ne saboda yadda cutar korona ta tsayar da fannin ilimi na shekara biyu.
Shafin intanet din ma’aikatar ilimi ne ya kirkiro da wannan sabon tsari da nufin zaburar da dalibai koyon ilimi, da karawa malamai karksashin koyarwa, wanda dukkan bangarorin biyu za su samu damar shiga shafin.
Adamu Adamu ya kara da cewa ma`aikatar ta hada kai da majalisar rijistar malamai ta Najeriya domin bai wa malamai masu rijista kawai damar shiga shafin yanar gizon
You must log in to post a comment.