Majalisar dattawa ta yi zama na uku a kan kudurin maida kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna zuwa cikakkiyar Jami’ar Birnin Kaduna, wato City University of Technology a turance.
Hakan dai, ya biyo bayan nazarin da kwamitin asusun tallafa wa manyan makarantu na majalisar dattawa a karkashin jagorancin Sanata Jibrin Barau ya yi a kan Kudurin da Sanata Shehu Sani ya kai.
Ana sa ran majalisar dattawa za ta tura kudurin zuwa ga majalisar wakilai domin su sanya hannu kafin a gabatar da shi a gaban shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu sannan ya zama doka.Bangaren ilimi dai na ci-gaba da samun kalubale a Nijeriya, musamman makarantun gaba da sakandare, wadanda ba wuya ma’aikatan su ke shiga yajin aiki saboda wasu bukatun su.