A yanzu haka Kudurin dokar kafa hukumar da za ta dinga kula da tsangayoyi da almajirai da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta musamman a jihohin da ke arewacin kasar nan ya
karatu na biyu a Majalisar Wakilan kasar.
Manufar kudurin ita ce samar wa masu karatun allo daraja da hanyar dogaro da kai ta yadda al`umma za ta daina kallonsu a matsayin jahilai saboda ba su yi karatun boko ba.
Hon Shehu Kakale shi ne ya gabatar da kudurin ya kuma shaida majiyarmu cewa babban burin wannan hukumar shi ne ta samar da matsayi da kima da mutunci ga karatun almajirci da tsangaya da makaruntun allo
Ya kara da cewar ba zai yuwu a ce wanda zai iya karatu da rubutu da Larabci ko ajami ko ya haddace Al’kur’ani sannan a ce mi shi jahili ba.