Home Labaru Ilimi Ilimi: Gwamnatin Sokoto Ta Biya Wa Daliban Kudin Jarrabawar NECO Da WAEC

Ilimi: Gwamnatin Sokoto Ta Biya Wa Daliban Kudin Jarrabawar NECO Da WAEC

1302
0

Gwamnatin jihar Sakkwato ta biya naira miliyan dari 3 a matsayin kudin jarabawar dalibai na kammala makarantar sakandari na WAEC da NECO na shekarar 2018 da 2019.

Kakakin ma’aikatan ilimi na jahar, Nura Bello Maikwanci, ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a  Sakkwato, inda ya ce gwamnati ta biya kudaden ne domin a sako sakamakon jarabawar daliban.

Bello Maikwanci,  ya shawarci daliban jihar da iyayensu, su kara hakuri saboda gwamnati na daukan duk matakan da suka dace domin tabbatar cewar an sako sakamakon jarabawar.An biya kudaden ne domin daliban da suka zana jarabawar da hukumar WAEC da NECO suke shiryawa, kuma ana sa ran a wannan ci gaba da aka samu, hukumomin za su saki sakamakon jarabawar nan bada jimawa ba.

Leave a Reply