Mahukunta a yankin Rio Grande do Sul da ke kudancin Brazil,
sun yi gargadi sake fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon yadda
madatsun ruwa ke cika da batsewa yayin da ake ci gaba da tafka
ruwan sama kamar da bakin-kwarya.
Akalla mutane 39 ne suka mutu a ambaliya da zabtarewar laka a kwanakin da aka shafe yanzu ana ruwa, sannan akwai kusan mutane 70 da suka bata.
Ko a ranar Alhamis din da ta gabata sai dai wata madatsar ruwan da ke samar da lantarki a kusa da birnin Bento Gon-cal-ves ta
ɓalle. Ana ci gaba da aikin ceto da samarwa mutane matsugunan wucin gadi.