Wata tankar mai ta fashe a jihar Gombe, inda ta yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutane goma, sannan ta kone motoci masu yawan gaske
Wani wanda abin ya auku a idon ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce tankar mai dauke da man fetur sun yi taho mu game ne da wata babbar mota wacce ta ke dauke da ruwa a babbar hanyar fita daga garin Gombe.
Wata kungiyar mai kai daukin gaugawa ta dauke gawarwakin mutanen zuwa wani asibiti mafi kusa. Ita ma hukumar kashe gobara na jihar Gombe na aiki domin ganin sun shawo kan wutar da ta ke ci.