Home Labaru If’tila’i: Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje 271 A Sanga

If’tila’i: Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje 271 A Sanga

854
0
If’tila’i: Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje 271 A Sanga
If’tila’i: Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje 271 A Sanga

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje masu tarin yawa a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.

Shugaban karamar hukumar Charles Danladi ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Afrilu, tare da cewa ruwa ya yi barna a garuruwa 6 da ke karamar hukumar.

Danladi ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da  manema labarai a Kafanchan, inda yace lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

Charles Danladi ya bayyana garuruwan da lamarin ya shafa wanda suka hada da Aboro da Sabon Gida da Ungwan Bera da Janda da Ungwan Goma  da kuma Kurmin Goro

.

Haka kuma shugabankaramar hulkukmar ya ce, ruwan ya dauke rufin wata makaranta, sannan an yi asarar wasu shaguna, amma babu wanda ya rasa ransa a sanadiyyar faruwar lamarin, sai dai akwai wadanda suka samu rauni, kuma tuni an garzaya da su  asibiti domin samun  kulawa.

A karshe Charles Danladi ya ce ya umarci daraktan ayyuka na karamar hukumar ya zagaya garuruwan da lamarin ya shafa domin gano asarar da aka yi, domin samin yadda za a taimakawa mutane da if’tila’in ya shafa.

Leave a Reply