Home Labaru Iftila’i: Gobara Ta Kona Filin Jirgin Saman Jihar Imo

Iftila’i: Gobara Ta Kona Filin Jirgin Saman Jihar Imo

233
0

Fasinjoji da ma’aikatan filin jirgin sama na Sam Mbakwe Cargo dake jihar Imo sun shiga cikin rudani lokacin da wani bangare na ginin filin jirgin ya kama da wuta.

Babu wanda ya san musabbabin gobaran, amma wata majiya daga filin jirgin ta bayyana cewa, ana gyara a babban dakin tarbar baki, inda dakin ya kone kurmus.

Wakilinmu ya bayyana mana cewa, kobarar ta kai awa daya tana tashi, inda ta fara tun da misalin karfe 2 da minti10 na rana.

Wutar ta tashi ne a babban dakin tarbar baki na filin jirgin saman wanda ake gudanar da aiki a cikinsa, ta yi barna sosai, amma duk da haka jami’an hukumar kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar.

Lokacin da aka tutubi kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Imon, Orlando Ikeokwu, ya bayyana cewa, ba su samu labarin lamarin lamarin a hukumance ba.