Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Idris Wase Ya Ce Wannan Ne Lokacin Da Zai Zama Kakakin Majalisar Tarayya

Mataimakin Kakakin Majalisar wakilai Idris Wase, ya yi fatali
da matsayar da APC da Bola Tinubu su ka ɗauka na bada
shugabancin shugaban Majalisar wakilai ga Tajuddeen Abbas
na Jihar Kaduna.

Idris Wase, wanda a yanzu shi ne Mataimakin shugvaban majalisar wakilai, ya ce shi ma yanzu lokaci ne da zai zama Kakakin Majalisar Tarayya.

Wase ya bayyana haka ne a masaukin baki na Transcorp Hilton da ke Abuja, inda ya ce shi ma ya ari salon da Bola Tinubu ya yi na ‘Emi lokon’, cewa shi ma yanzu lokacin sa na.

Ya ce dole jam’iyyar APC ta bi tsarin da dokokin tsarin mulkin Nijeriya ya shimfiɗa, ta yadda za su tabbatar da cewa ba a maida yankin Arewa ta Tsakiya tamkar saniyar-ware ba.

Exit mobile version