Mutum uku sun rasa rayukan su a garin Takum da ke jihar Taraba sakamakon wata guguwa da ta faru sau biyu cikin kwana biyu.
Rahotanni sun ruwaito wani mazaunin garin Mallam Maiwada Takum na cewa guguwar ta soma faruwa ne da yammacin ranar Talata inda ta yi gagarumar ɓarna ga gidaje da makarantu da ofisoshi.
Takum ya ƙara da cewa da farko an yi mamakon ruwan sama daga bisani kuma aka yi guguwa mai ƙarfi da ta shafe fiye da sa’a ɗaya da rabi tana zagawa.
Shi ma wani mazaunin garin, Yakubu Adamu, ya bayyana cewa guguwar ta yi matuƙar ɓarna inda ta salwantar da gidaje da rayuka.
Babban mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Emmanuel Bello ya ce gwamnan Agbu Kefas ya higa garin domin duba irin ɓarnar da guguwar ta yi.
An kuma bayar da rahoton mutuwar mutum ɗaya da jikkatar wasu da dama sakamakon tashin guguwa da ta lalata gidaje fiye da 100 a yankin Agbashi da ke ƙaramar hukumar Doma a jihar Nassarawa.
Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, John Bako-Ari ne ya tabbatar da lamarin inda ya ce guguwar ta tashi ne ranar Talata da yamma.