Home Labaru Kasuwanci Ibtila’i: Gobara Ta Tafka Barna A Kasuwar Balogun Da Ke Legas

Ibtila’i: Gobara Ta Tafka Barna A Kasuwar Balogun Da Ke Legas

930
0

Wata mummunar gobarar da ta shi a birnin Legas, ta yi sanadiyyar tafka asarar tarin dukiya ta miliyoyin naira.

Gobarar dai ta soma tashi ne a wani bene mai hawa 6 a layin Oluwole da ke kasuwar Balogun, yayin da wata gobarar ta kone shagunan da ke bene mai hawa na 3 a layin Dosunmu da ke kasuwar.

Ya zuwa yanzu dai, babu karin bayani a kan musababbin tashin gobarar, sai dai hukumar bada agajin gaugawa ta jihar Legas ta sanar da shawo kan ta, bayan shafe tsawon lokaci jami’an kwana-kwana su na gwagwarmaya.