Wata kotu a Birtaniya ta umurci tsohon gwamnan jihar Delta
James Ibori ya biya kudin da ya kai fam miliyan 130 da ya yi
sama da fadi da su a lokacin da ya Mulkin jihar.
An dai yanke wa James Ibori hukuncin zaman gidan yari a Birtaniiya ne a shekara ta 2012, sakamakon kama shi da laifin halasta kudaden haram da zamba cikin aminci.
Daga nan ne masu binciken kudi daga ofishin yaki da muggan laifuffuka na Birtanniya su ka fara daukar matakan kwace abubuwan da ya samu da kudaden da ya yi kwanciyar magirbi a kai.
Yayin zaman kotun na ranarLitinin da ta gabata, masu binciken sun zargi Ibori da tara kudade masu dimbim yawa, inda alkalin kotun ya umurce shi ya maida wa gwamnatin jihar Delta sama da Fam miliyan 100.
Haka kuma, kotun ta umurci lauyan tsohon gwamnan mazaunin Birtaniya Badresh Babulal Gohil, ya maida kudaden da yawan su ya kai sama da Fam miliyan 28.