Home Labaru Hushpuppy: Matakin Dakatar Da Abba Kyari Izina Ce Ga ‘Yan Sanda –...

Hushpuppy: Matakin Dakatar Da Abba Kyari Izina Ce Ga ‘Yan Sanda – Cp Muhammad Wakil

90
0

Tsohon Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano CP Muhammad Wakil mai ritaya, ya ce dakatar da DCP Abba Kyari tare da kaddamar da bincike a kan sa shi ne matakin da ya fi dacewa a dauka domin sanin gaskiyar lamarin.

Hukumar kula da harkokin ‘yan sanda dai ta dakatar da Abba Kyari daga aikin ɗan sanda, sakamakon zargin hannu a wata damfara da Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka FBI ke yi ma shi.

Idan dai ba a manta ba, Hukumar ta ɗauki matakin dakatar da DCP Abba Kyari ne, bayan shawarar da shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba ya bada.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, CP Muhammad Wakili, ya ce hakan zai iya zama izina ga sauran jami’an da ke tunanin kamanta halayya makamanciyar wannan.