Home Labaru Hukuncin Kotu: Abdulmumin Jibril Ya Maida Martani

Hukuncin Kotu: Abdulmumin Jibril Ya Maida Martani

427
0
Abdulmumin Jibrin, Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Mazabar Kiru Da Bebeji A jihar Kano
Abdulmumin Jibrin, Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Mazabar Kiru Da Bebeji A jihar Kano

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru da Bebeji a jihar Kano Abdulmumin Jibrin, ya maida martani a kan hukuncin kotun koli da ta soke zaben sa, inda ya ce hukuncin abin al’ajabi ne kuma bai yi daidai da tsarin shari’a ba.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne, kotun ta kwace kujerar dan majalisar, sannan ta bada umarnin gudanar da sabon zabe.

Yayin da ya ke maida martani, Jibrin ya ce hukuncin mutanen Kiru da Bebeji shi ne sabunta yardar da su ka ba shi domin wakiltar su a majalisar tarayya.

Ya ce a matsayina na musulmi nagari, dole ne ya yi imani da Allah, kuma ya yarda cewa duk abin da zai faru a karkashin ikon sa ne. Sai dai ya ce babu shakka bai aminta da hukuncin kotun daukaka kara ba, kuma a matsayin sa na wanda aka raina a dimokradiyya, ya na kira ga magoya bayan sa su koma domin sake zaben, domin har yanzu ya na da tabbacin shi ne zabin mutanen Kiru da Bebeji.